Yaki da ′yan ta′adda a Yammacin Afirka | Siyasa | DW | 02.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yaki da 'yan ta'adda a Yammacin Afirka

A kokarin tinkarar matsalar sojoji daga kasashen Afirka da Amirka da Turai suna gudanar da atisaye a yankin, a wani yunkuri na ko dai hana kai hare-hare ko kuma kai daukin gaggawa idan bukatar haka ta taso.

Atisayen da ake wa lakabi da "Flintlock" da kuma ake yi tun shekaru 10 da suka wuce, a bana dakarun sojin za su yi shi ne a kasashen Senigal da Mauritaniya daga 8 zuwa 29 ga watan nan na Fabrairu.

Baya ga Amirka da Jamus, akwai kuma sojojin 1700 daga kasashen Yammaci da Arewacin Afirka wadanda suka hada da kasashen Alejeriya, Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritaniya, Marokko, Nijar, Najeriya, Senigal, Afirka ta Kudu da kuma Tunisiya. Inda za su hadu da takwarorinsu daga kasashen Yamma kamarsu Italiya, Faransa, Netherland, Spaniya da Birtaniya sai kuma Kanada, wadanda za su shiga cikin atisayen da ake wa lakabi da "Flintlock", inji rundunar Amirka ta Africom da ke da mazauni a birnin Stuttgart na kasar Jamus, wadda kuma tun daga 2008, take kula da aikin sojojin Amirka a Afirka.

A lokacin da yake bayyana muhimmancin atisayen Manjo Nathan Broshear, na rundunar Amirka ta Africom da yaki a nadi muryarsa, ya jaddada muhimmancin kawancen yaki da ta'addanci musamman a Yammacin Afirka da ayyukan ta'adda ke karuwa.

Shi ma Birgediya-Janar Zakaria Ngobongue daga kasar Chadi da a bara ya shiga cikin atisayen na "Flintlock" tsawon makonni uku, ya ce kasancewa kungiyoyin 'yan ta'adda na kai hare-haren tsallaken iyakokin kasa, ba zai yiwu hukumomin tsaron a kasashen yankin su ki hada kansu don tinkarar 'yan tarzoman ba. Shi ma Birgediyan da ya ki a dauki muryarsa, ya ce har yanzu babu cikakken hadin kai na kasa da kasa a yakin da ake yi da ta'ada a Yammacin Afirka da kuma yankin Sahel.A halin ma da ake ciki wasu kasashen da a da ba sa fuskantar barazana daga kungiyoyin 'yan ta'adda, yanzu kahaka sun shiga taskar 'yan tarzoma. Senigal da a bana za a gudanar da atisayen sojojin kasa da kasa, na daya daga cikin kasashen da ke fuskantar hadari na 'yan ta'adda. Henry Cissé shi ne kakakin ma'aikatar cikin gidan Senigal ya yi karin haske.

Ya ce: "Ba za mu iya cewa ba matsaloli ba. Ko shakka babu ana cikin wani hali mai tsoratarwa a yankin baki daya, ciki har da kasar Senigal. Ba za mu iya kawar da ido daga wannan ba. Akwai barazanar kai hare-hare, saboda haka dakarun tsaro ke cikin shirin ko-takwana."

Don haka Cissé ya yi maraba da atisaye da cewa, a kullum suna maraba da taimako daga kasashen duniya wajen kara karfin sojojinsu. Ya kara da cewa hare-haren da aka kai a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso a makonnin bayan nan, ya kara musu azama dangane da matakan yaki da ta'addanci.

Ya ce: "Kawo yanzu an gudanar da taruka a kan batutuwan da suka shafi matakan riga-kafin aikin ta'addanci, inda masana da dama daga kasashen yankin suka halarta. Sai dai har yanzu hadin kan ba shi da karfi sosai."

A baya-bayan nan Senigal, ta kara yawan sojojinta da ke sintirin kan iyakokinta, musamman tsakaninta da Mali da kuma Mauritaniya.

Sauti da bidiyo akan labarin