1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Fafaroma Francis a Mexiko

Yusuf BalaFebruary 15, 2016

Shugaban darikar ta Katolika ya diga allurar rigakafin wannan cuta me nakasa yara a bakin wani yaro da Angelica Rivera matar shugaban kasar ta Mexiko ta dauka.

https://p.dw.com/p/1HvRR
Mexiko Papst Franziskus von Pena Nieto empfangen
Fafaroma Francis na musabaha da yara tare da shugaban kasar Mexiko da mai dakinsaHoto: Reuters/M. Rossi

Fafaroma Francis ya kaddamar kamfe na yaki da cutar Polio a kasar Mexiko a ranar Lahadi, bayan ziyarar da ya kai wani asibitin kananan yara a birnin Mexiko a ziyarar da ya ke a wannan kasa. Da yake jawabi ga taron manema labarai a yammacin ranar Lahadi Frederico Lombardi, mai magana da yawun fadar ta Vatican ya ce shugaban darikar ta Katolika ya diga allurar rigakafin wannan cuta me nakasa yara a bakin wani yaro da Angelica Rivera matar shugaban kasar ta Mexiko ke dauke da shi. Abin da ke nuna fara kamfe na yakar wannan cuta a cewar Lombardi .

"Abin sha'awa a nan shi ne Fafaroma ya kaddamar da kamfe kan wannan cuta a wannan rana, sannan ya yi kyautar magunguna na wannan cuta ta Polio abin da ke nuna cewa an kaddamar da yaki da wannan cuta a wannan shekara."

Har-ila-yau a jawaban da ya gabatar yayin wani taron addua da ya jagoranta da mabiya kimanin 300,000 da suka halarta a ranar ta Lahadi, Fafaroma ya bukaci al'ummar wannan kasa da su gujewa ribatar shedan da ke sanyawa wasunsu basa daukar dillancin kwayoyi da kisan al'umma a matsayin abin da ba laifi ba saboda kekashewar zuciya.