Yaki da Muggan Laifuka | Masu Yaki da Muggan Laifuka | DW | 03.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Yaki da Muggan Laifuka

Yaki da Muggan Laifuka

A kokarinmu na ilimantar da matasa kan muhimmancin kiyaye miyagun ayyuka, zamu gabatar muku da kasha na biyu na zubin "'yan ra'ayin rikau.

Ranar Juma’a (04-12-2015) Zamu kawo muku kashi na biyu na shirinmu na "Yaki da muggan laifuka, 'yan ra'ayin rikau". A wannan wasa namu matasan 'yan sandan Jibrin da Binta na kokarin gano musabbabin mutuwar Zahra Kasim, wacce ta kai harin kunar bakin wake a wani rukunin kantuna. 'yan sandan dai na kokarin kama shugaban kungiyar 'yan tayar da kayar baya mai suna Karabkiya da ke sanya matasa ayyukan tarzoma. Shin ko ya na da hannu a harin na kunar bakin wake? Sai ku kasance da mu don jin yadda zata kaya a wannan kashin mai taken "Abin ya wuce tunani".

Sauti da bidiyo akan labarin