Yaki da matsalar cin hanci a Najeriya | Siyasa | DW | 22.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yaki da matsalar cin hanci a Najeriya

Sakamakon yadda annobar cin hanci da karbar rashawa take neman rusa Najeriya, ya sa mahukunta shirya gudanar da babban taron kasa domin nazarin matsalar.

Dubban miliyoyin daloli ne dai ake zaton an badda. An kuma Ambato badakala a masana'antar man fetur din da kasar ke takama da ita , an ma ci kudi na yan fansho da matattu, sannan aka kai ga dauri irin rainin wayo duk dai a wani abun dake nuna alamar kazancewar matsalar cin hancin da sannu a hankali ke barazanar gurgunta al'amuran tarrayar Najeriya.

Matsalar kuma dake kara tada hankali a ciki da wajen tarrayar Nigeria in da mahukuntan kasar ke cigaba da bayani kan miliyan dubu kusan dari biyar din da ake zaton an sace a karkashin tsarin demokaradiyar kasar ta Najeriya.

Abun kuma da yanzu haka ya tilasta shirya wani taro na musamman domin tunkarar annobar a bangaren gwamantin kasar da tace tura ta kai bango kuma hakurin ta na iya wuya.

Cikin kasa da tsawon wattani shidan da suka gabata dai an fuskanaci jerin badakalolin da suka tada hankula kuma ke nuna alamun gazawa a bangaren mahukuntan da a baya ke ikirarin taunar tsakuwa ga batun cin hancin.

Alal misali dai jamian tsaro dama hukumomin nigeriar sun kau da ido sun kyale sulalewar shugaban kwamitin binciken fanshon gwamantin tarrayar kasar da ake zargi da wasoso da kusan naira miliyyan dubu dari biyar duk da umarnin tabbatar da kamoshin da majalisar dattawar ta kai ga yi.

Plakate gegen Korruption gibt es überall – doch oft sind sie wirkungslos Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 29. Oktober 2010 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Abuja, Nigeria

Abun da kuma a cewar Hon Jagaba Adams Jagaba dake zaman shugaban kwamitin yaki da batun cin hanci a majalisar wakilan Najeriyar yasa da kamar wuya ga gwamantin ta iya wani tasiri a kan batun.

Sata ta kamo sata ko kuma wasa da hankalin al'umma dai ya zuwa yanzu ana kallon rikon sakainar gwamantin a matsayin alama ta rashin gaskiya ga gwamantin da ake zargi da daure gindi da barayin kasar ta Najeriya.

Alal misali dai majiyoyi sun ce a cikin jirgin gwamantin kasar akai wa shugaban yan fanshon da ake nema rakiya ya bar kasar,

Sannan kuma har yanzu an gaza aiwatar da jerin rahotannin kwamitoci daban daban da suka tanaji hukunci mai tsanani ga jami'ai da ragowar yan kasar da ake zargi da kokarin daka wawa cikin rumbun al'umma.

To sai dai kuma a cewar dr Shamsudden Usman dake zaman ministan tsare tsaren tattalin arzikin kasar ta Nigeria salon yakin gwamantin kasar ba irin na kame barayi ne ba.

Abun jira a gani dai na zaman tasirin sabuwar dabarar ga kokarin kawo karshen matsalar da sannu a hanakali ke zaizaye tasirin demokaradiyar kasar a zukatan alummar ta.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin