1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da masu kamun kifi ta haramtattun hanyoyi a Ghana

Maxwell Suuk/YBSeptember 30, 2015

Mazauna garin Winneba a Ghana sun koka da masu amfani da haramtattun dubarun kamun kifi, suna kuma ci da gumun kananan yara.

https://p.dw.com/p/1Gg9Y
Ölboom in Ghana
Hoto: DW/G. Hilse

Wasu al'ummomi da ke zama fitattu wajen sana'ar kamun kifi da kasuwancinsa ta hanyoyi da aka gada tun kaka da kakanni a garin Winneba, wani yanki da ke a tsakiyar kasar Ghana, sun koka kan yadda wasu ke zuwa suna amfani da wasu dabarun kamun kifi irinsu amfani da hasken fitila ko sanadirai suna hana musu hanyar samun abinci. Yayin da a bangare guda kuma suke ci da gumun kananan yara.

Wata mata mai shekaru 54 da ake kira Nyaniba a kofar gidanta tana gasa kifi a garin na Winneba, daya daga cikin garuruwa da suka yi fice a sana'ar kamun kifi a tsakiyar kasar ta Ghana, ta ce kasuwancin na kifi da take yi tun tana da shekaru 24 a yanzu ba ya sama musu kudaden shiga.

"A lokutan baya mu da muke sana'ar sayar da kifi mu attajirai ne, amma yanzu kasuwancin ya durkushe gashi ina da yara, in biya musu kudin makaranta ya zama aiki. Matsalar dai ita ce masu amfani da haske cikin dare suna bin gefen teku su kwashe kifin, ya kamata su daina."

Ölboom in Ghana
Mata na taka rawa a kasuwar kifi a GhanaHoto: DW/G. Hilse

Duka dai, masu kamun kifin ne ko masu kasuwancinsa a wannan yanki na Winneba na kokawa ne da wadannan masu sana'ar ta kamun kifin ta hanyoyi da suka saba wa doka, alal misali sukan yi amfani da sinadarai su zuba a teku ko su yi amfani da hasken fitila su tattaro kifin ko dai wasu dabarun da doka ta hana.

Koma baya ga masunta na asali

A gefen teku ruwa ne ke kai kawo, ya bugi gaba ya koma, masu su na baza koma dan kama kifi. Clement Offosu na daya daga cikin masuntan da ke shirin baza komarsa ya kuma koka ga wadannan masu kamun kifi da ke amfani da hasken fitila.

"A lokutan baya kamun kifi na da dadi amma yanzu babu komai a teku wannan masu fasakauri ba bu abin da suke sai illata mana sana'a."

Wannan dai kamun kifi da ya saba da na dauri ta wannan hanya mai illa ga muhalli a cewar Khalid Sualih shugaban ma'aikatar kamun kafin a yankin Arewacin Ghana masu irin wannan mugun aiki doka ta yi tanadin dauri a garesu.

"Ya saba wa doka a kama mutum yana amfani da wasu hanyoyi da kan gurbata muhalli wajen kamun fili hada ma da amfani da haske da ma wasu na'urori wajen kamun kifin duka wadannan sun saba wa doka."

Symbolbild Moderne Sklaverei Menschenhandel Ghana
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Ridley

Wata kididdiga dai ta bayyana cewa kashi 60 cikin 100 na sinadaran Protein da ake samu daga abinci a kasar ta Ghana na fitowa ne daga kifi, sannan akalla cinikin da ake samu idan aka fitar da kifin zuwa waje ana iya samun dalar Amirka miliyan 254 , abin da kuma ke samun koma baya. Sai dai a cewar Mista Sualih da yawa cikin masu kokawa da wannan kamun kifi da ya saba wa ka'ida suke yi ko su dauki nauyi.

Ci da gumin yara a sana'ar kamun kifi

Yara ne a gabar teku suke aikin na su, da komarsu a hannu. Ganson Emmanuel daya daga cikinsu ya ce idan ba wannan sana'a to ba rayuwa.

"Ina samun kudi ta hanyar kamun kifi, na kan dinka wa kaina tufafi kai da duk abin da nake bukata, ba na jin zan iya rayuwa idan babu wannan."

Bincike dai ya tabbatar da cewa bayan ga fannoni na noman koko da hakar zinare, sana'ar ta kamun kafi na daya daga wadanda ake ci da gumin yara a kasar ta Ghana, abin da kuma ya saba wa dokar kasar da ma dokar kasa da kasa.