1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sanin matsayi a kan cutar AIDS ko SIDA

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 29, 2018

A ranar daya ga watan Disamba ne ake gudanar da bukukuwan waayar wa da al'umma kai kan yaki da kwayar cuta mai karya gaarkuwar jiki wato HIV/AIDS ko kuma SIDA.

https://p.dw.com/p/398pn
Schweiz Labor Symbolbild
Hoto: picture-alliance/KEYSTONE/G. Bally

A ranar daya ga watan Disambar da ke tafe ne, ake cika shekaru 30 da bayyanar cutar HIV/AIDS ko kuma SIDA. Cutar da za a iya caewa an cimma nasara da irin fadakarwar da ke yi a kanta, a fagen yaki da yaduwarta a duniya. Miliyoyin mutane sun rasa rayukansu, yayin da wasu tarin miliyoyin kuma ke karbar magani. Taken bikin na bana dai shi ne "San Matsayinka ta Hanyar yin Gwaji."