Yaki da cutar AIDS ko SIDA a Senegal | Zamantakewa | DW | 22.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yaki da cutar AIDS ko SIDA a Senegal

Masu fafutukar yaki da Cutar AIDS ko SIDA a Senegal sun bayyana gamsuwa kan yadda hukumomin a kasar ke yaki da cutar, abinda suka ce ya haifar da nasarori a yakin.

Duk da cewa kasar Senegal na daga cikin kasashe da suke fadi tashi wajen neman gina tattalin arzikin kasa, cutar SIDA ba ta samu gindin zama ba saboda irin matakai da hukumomi suka dauka wajen ganin an yake ta.

Tun a shekarar 1986 ne dai hukumomin kasar suka kafa hukumar yaki da cutar SIDA da ake kira National Program for the Fight against AIDS a turance inda kuma a shekara ta 2002 aka sakewa hukumar suna zuwa National Council for the Fight against AIDS.

Samar da wannan hukuma tare da bata dukkanin goyon bayan da ya kamata shi ne musabbabin samun nasarar yaki da wannan cuta a tsakanin al'ummomin kasar ta Senegal wanda aka kiyasce yawansu ya kai kusan miliyan goma sha hudu a kididdigar da aka yi a shekara ta 2012.

Namibia Protest Frauen Diskriminierung HIV

Fafutukar yaki da cutar AIDSS ko SIDA na karuwa a kasashen Afrika

Wannan ya sa kungiyoyi masu fafutukar yaki da cutar SIDA ko kuma HIV/AIDS bayyana gamsuwa kan yadda hukumomi a kasar Senegal ke yaki da cutar abinda suka ce shi ne ke haifar da nasarori na magance yaduwar cutar a kasar.

A cewar kungiyoyin, irin matakai na wayar da kai da kuma samar da magunguna ga masu fama da cutar da kuma ilmantar da mutane kan nuna kyama ga masu dauke da ita sun taimaka gaya wajen rage yaduwar cutar musamman tsakanin matasa .

Madam Fatuo Ndiye shugabar wata kungiya ce mai yaki da yaduwar cutar a kasar Senegal.

Ta ce ''Muna jinjinawa hukumomi a kasar nan saboda yadda suka tashi haikan wajen yaki da wannan cuta hakan ya sa an samu nasarar shawo kan yaduwar cutar musamman a wuraren da ta fi kamari kamar Mbur da Dakar. Fatan da mu ke yi dai shi ne mutane su daina nuna kyama ga masu cutar saboda cuta ce kamar kowace irin cuta. Mutanen kasar nan na yin biyayya ga shawarwarin da ake ba su na yadda za su kare kawunansu.”

Bildergalerie Geschichte von HIV/AIDS

Gwaji don sanin matsayin mutum kan cutar AIDS ko SIDA na rage yaduwarta

A nasu bangaren hukumomi da ke yaki da wannan cuta na danganta samun nasarar da hadin kan da al'umma ke ba su da kuma irin muhimmiyar rawa da kafafan yada labaran kasar ke takawa wajen fadakar da al'umma.

Wannan ya sa na tambayi Babacar Niang shugaban gidan Talabijin na tauraron dan Adam da ake kira Al-Madina kan irin gudumowar da kafafan yada labarai ke bayarwa a yaki da cutar SIDA a kasar Senegal sai ya ce:

“Muna fadakar da su, muna nuna musu yadda za su kare kawunansu. Wannan hakki ne da ya rataya a wuyanmu saboda cutar SIDA na gurgunta tattalin arzikin kasa da kuma gurgunta harkokin kiwon lafiya. Muna kira ga mutane a rungumi masu fama da wannan cuta tare da nuna kauna ta haka ne kawai za su samu yin walwala tsakanin ‘yan uwansu mutane.”

Kungiyoyin yaki da wannan cuta da ma sauran talakawa sun nemi sauran kasashe da ke makobtaka da kasar ta Senegal da su dauki irin wadanan matakai don tabbatar da nasarar yaki da yaduwar cutar a nahiyar Afirka inda ta fi samu gindin zama.

Mawallafi: Amin Sulaiman Muhammad
Edita: Mohammed Nasiru Awal/Ahmed Salisu