Yaki da cin hanci na son gyara a Najeriya | Siyasa | DW | 22.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yaki da cin hanci na son gyara a Najeriya

A cewar masu zanga-zangar adawa da salon yaki da cin hanci da rashawa a Abuja, har yanzu akwai masu halin bera da ke barna a gwamnatin Shugaba Buhari, duk da ikirarin da take na yaki da cin hanci da rashawa.

A Najeriya wasu kungiyoyin kare hakkin jama'a sun gudanar da zanga-zanga a kan matsalar yaki da cin hanci da rashawa da suka ce na tafiyar hawainiya tare da bukatar Shugaba Muhammadu Buhari ya kara azama da daukan matakin da ya dace, musamman zargin ci gaba da cin hanci a wasu ma'aikatun gwamnati da ya zarta Naira biliyan dubu.

Masu zanga-zangar sun rinka rera takensu a lokacin da suka yi tattaki zuwa ofishin hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa EFCC kan sako-sako da ma wasan da suka ce gwamnati na yi da batun cin hanci da rashawa da suka ce duk da yakin da wannan, mummunar dabi'a har yanzu akwai masu halin bera da ke barna a gwamnatin. Kwamared Aliyu Isa Isa Abubakar ya bayyana abin da cewa na daga masu hankali.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria (cc-by-sa/Shiraz Chakera)

Masu rike da madafun ikon ma ana zargin wasu da karkatar da dukiyar talakawa

Sun dai samu tarba daga jagoran hukumar EFCC Malam Ibrahim Magu wanda ya maida martani a kan bukatun nasu: "Ba sani ba sabo duk wanda ya yi za'a yi masa, mu muna son kowa ya taimaka domin wannan abin ba zamu yi mu kadai ba."

To sai dai basu samun irin wannan tarba ba a lokacin da suka tunkari fadar shugaban Najeriyar, inda jami'an ‘yan sanda suka yi masu kawanya dama toshe hanyar shiga, an kai ga dauki ba dadi da su daga baya wani jami'in a fadar Godwin Uja ya karbi sakon takarda tare da kin cewa uffan.

Daya daga cikin matan da suka yi zanga-zangar Fatima Almu ta ce cin hanci na shafar rayuwarsu sosai a Najeriya.Ga Ibrahim Garba Wala kuwa na kungiyar kokarin ceto Najeriya ya ce hali da ake ciki da takaici.

Irin hali na sako-sako da yaki da cin hanci da rashawa a Najeriyar dai na zama babban kalubale a wannan gwamnati sanin cewa batun na zama daya daga cikin alkawuran da ta yi wa al'ummar kasar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin