Yaki da cin hanci da rashawa a kasar Cameroun | Siyasa | DW | 29.01.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yaki da cin hanci da rashawa a kasar Cameroun

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a kasar Cameroun ta shiga gadan gadan capkar mutanen da ak a samu da wannan leffika

Kasar Kamaru ta shiga gadan gadan, a yaki da cin hanci da rasahawa, wannan ya biwo bayan kiddidigar da kungiyoyin kasa da kasa su ka gudanar a shekara da ta gabata, wacce a sakamakon ta, Kamaru ta kasance jagoran a dunia ta fannin cin hanci da karbar rashawa.

A cikin wannan saban hoba sarma, hukumomin Kamaru, sun bada sanarwar tsige da dama daga mutanen da a ka samu da hanu dumu dumu cikin al´amarin, kamo daga jami´an tsaro jami` an Kostom ko Duwan, da dai sauran mutane, da hakin tattara kudaden jama´a, ya rataya a kan su, kuma suke yi masu rabda da ciki.

Kungiyin kasa da kasa, da kafofin bada tallafi na dunia, da ke bi sau da kafa wannan yaki da cin hanci da rashawa a Kamarum, sun nuna shaku.

Su na masu zargin gwammnati, da daukar matakan hukunci kadai, ga wanda basu da iyaye a gidin murhu,kazalika sun cika yin magori wasa kanka da kanka, ta hanyar anfani da kafofin sadarwa, da zumar nuna ma dunia cewar Kamaru ta daura damara yaki da cin hanci da karbar rashawa.

Kungiyar Transparency International, ta yaba saban matakin da hukumar yaki da cin hanci da karbar rashawa ta Kamaru ta dauka, to amma a cewarv ta har yanzu da sauran rina kaba ko da shike hausawa klan ce wanda zai sama ya hau faifai, ya dan ci gaba.

A nasu bangare al´ummomin kasa suma, na daukar wannan mataki tamkar bulla,don burge kasashen ketare da sauran kungiyoyi da su ka kafa wa kasar kafan zuka a kan maganar rashi adalci.

Sun tuhumi hukumar yaki da cin hanci da karbar rashawa da aikata wani saban sallon sama da fadi da dukiyar jama´a, ta hanyar anfani da kashi 50 bisa 100 na kuddaden da ta ke karba daga wajen jama´a.

A makon da ya gabata kimanin shugabaninkampanoni 20 ne gwamnati ta sallama dukan su bayan bincike ya gano cewra su da hannu a cikin harakoki cin hanci da karbaer rashawa a trafiyar da harakoki kampanonin su.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya da kansa ya ja hankuulan al´umar kasar a wani jawabi a game da matakin ba gudu ba ja da baya a yunkurin kakkabe makarba rasahawa daga harakoki mulkin kasa.

Jim kadan bayan wannan sallama, shugaban rundunar jamai´an Kustom na kasa ya bada labarin cewa kashi daya bisa 4 na ma´aikatan Kustom su 2000 a kasar Kamaru, sun yi kaurtin suna ta fannin karbar rashawa, kuma nan bada jimawa ba doka zata hawa kann su a cewar sa.

Jikadan kasdar Amurika a Yaounde babban birnin kasar ya hurta cewa, bayyana sunayen masu karbar rashawa kokuma fida su daga aiki,bai da wani tasiri, matakin da ya dace a cewar sa shine na gurfanar da su gaban kotu domin ta yanke masu hukunce da ya dace, idan gwamnatin Kamaru ta aikata hakan, to kasashen dunia za su shaidi cewa, ba da wasa ta ke ba.

Masu kula da harakokin da ke kai su zo a kasar, na danganta wannan saban fadi ka tashi, da siyasa don birge tawagar asusun bada lamani na dunia, da ta fara ziyara aiki ranar juma´a a wannan kasa.

Kila ta wannan hanya Kamaru zata samu nasara shiga, sahun kasashen Afrika matalauta da za su ci gajiyar yafe bassukan da kasashen masu hannu da shuni su ka tamnbayo su.

 • Kwanan wata 29.01.2006
 • Mawallafi Yahouza
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu22
 • Kwanan wata 29.01.2006
 • Mawallafi Yahouza
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu22