Yaki da cin hanci da rashawa a Iraki
December 8, 2014Talla
Al-Abadi ya ce gwamnatinsa a tsaye ta ke don yakar cin hanci ko da kuwa hakan ne zai sanadin rayuwarsa inda ya kara da cewar tuni ma suka fara bankado wasu shafaffu da mai kuma za su yi kokarin ganin sun fuskanci hukunci.
A karshen watan da ya gabata ne dai firaministan na Iraki ya ce wani bincike da aka gudanar ya gano cewar akwai ma'aikatan bogi dubu 50 da ya gada a rundunar sojin kasar wanda ake fidda albashi da sunansu.
To sai dai wanda ya gada din Nuri al-Maliki a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na AFP dazu ya musanta batun ma'aikatan na bogi da mahukuntan Irakin na yanzu suka ce sun gada daga gwamnatin da ya jagoranta.