1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da cin hanci a Najeriya

Ubale Musa/AHJuly 8, 2016

Gwamnatin Najeriya ta dauki hayar karin wasu lauyoyi har guda 80 domin kara karfin yakin da cin hanci.

https://p.dw.com/p/1JM03
Nigeria Abuja Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Krumm

Batun na yakin hanci dai na zaman daya a cikin ukun da gwamnatin 'yan sauyin ta alkawarta bayan nasarar zabe sama da shekara guda. Duk da cewar dai ta yi nasarar kamawa kama daga tsofaffin manyan sojoji ya zuwa masu takama da sana'a ta siyasa, daga dukkan alamu ana share shekara guda cikin hudu ba tare da kai wa ga tabbatar da hukunci daya ba kan kowa.

Tabbatar da hukunci a kan masu laifukan cin hanci

Tafiyar hawainiyar da ake ta'allakawa da gazawa ta kwarewa a bangaren lauyoyi na gwamnatin gami kuma da rashin isassun alklai sannan uwa Uba tsarin shari'a na kasar dai daga dukkan alamu na neman zama karfe a kafa ga kasar da ke cikin matsi na tattali na arziki amma kuma suka gaza kai wa kan dubban miliyoyin nairorin da suka yi nasarar ganowa a hannu na barayin.Abin kuma da ya kai ga gwamnatin kasar sake dabara tare da daukar hayar wasu lauyoyi masu zaman kansu har guda 80 domin karin karfin yakin.

Nigeria Gerichtshof in Abuja
Hoto: DW/U. Musa

Karin Lauyoyin zai taimaka wajen yaki da cin hanci a Najeriya

Ana dai sa ran lauyoyin da mafi yawansu ke zaman kwarraru a cikin yakin za su hadu da lauyoyi na gwamnatin inda za a sake raba su zuwa kungiyar mutum Hudu kan ko wane a cikin manyan shari'un cin hancin kasar.Babban buri dai a fadar ministan shari'ar kasar Abubakar Malami na zaman kai wa ga tabbatar da hukunci kan kowa a cikin lokaci na kankane.

Karikatur raffgierige Politiker in Nigeria
Hoto: DW/Abdulkareem Baba Aminu