Yaki da cin hanci a Hong Kong | Labarai | DW | 23.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaki da cin hanci a Hong Kong

Kotu a Hong Kong ta yanke wa wani hamshakin dan kasuwa hukuncin daurin shekaru biyar a gidan kaso sakamakon kama shi da laifin ba da cin hanci da rashawa.

Shi dai wannan hamshakin dan kasuwa mai suna Thomas Kwok, dan shekaru 63 da haihuwa, an same shi da laifin bada cin hanci ga tsofon sakataran gwamnatin kasar Rafael Hui, dan shekaru 66 da haihuwa wanda shi ma yake daure a gidan kaso na tsawon shekaru bakwai da watanni shida, bayan da ya amsa laifinsa na karbar cin hanci na kudi dallar Hong Kong milian 34 kwatankwacin Euro Milian 2,8 a matsayin kyauta ko bashin da babu wata riba.

Hong Kong dai na kokarin kare mutuncin ta ne, ta hanyar bunkasa arzikinta, wanda hakan ba zai samu ba muddin akwai yanayi na cin hanci da karbar rashawa da ke hana ruwa dugu ga ci-gaban kasashe da dama a duniya.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo