1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da badakalar cin hanci a Ruwanda

Abdul-raheem Hassan
October 11, 2017

Yayin da gwamnatin Ruwanda ta soma bankado batun cin hanci da almundahana a tsakanin ma'aikata, wani rahoton kungiyar kare hakin dan Adam ta HRW ya zargi sojojin kasar da azabtar da mutane.

https://p.dw.com/p/2lZhW
Ruanda Präsident Paul Kagame
Shugaban Ruwanda Paul KagameHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Senne

A baya dai Ruwanda ta zama zakaran gwajin dafi a cikin kasashe masu karancin cin hanci da rahawa a tsakanin kasashen Kudu da Sahara. Wannan kuwa baya rasa nasaba da yunkurin Shugaba Paul Kagame na nuna ba sani ba sabo a yaki da cin hanci a kasar. Kusoshin gwamnati da dama sun shiga hannun shari'a.Sai dai da ci gaban zamani wasu mukarraban gwamnatin sun yi nisa wajen iya wawuran dukiyar kasa da ma iya karesu a kasashen waje. Amma Janarl John Bosco Mutanga da ke zama mai gabatar da kara a kasar ya ce ma'aikatarsa ta kaddamar da bincike mai tsanani.

Kaddamar da bincike a ma'aikatun ruwanda

Diane Rwigara
'Yar Adawar kasar Ruwanda Diane RwigaraHoto: DW/E. Gatanazi

"Akwai manyan shugabanni da ke da hannu a harkokin cin hanci, da cuwa-cuwa, da karkata dukiyar kasa da gangan da sunan gina kasa. A matsayina na mai shigar da kara, mun yi amannar cewa akwai bukatar a gurfanar da irin wadannan mutane. Muna da cibiyoyin gwamnati da dama da zamu bincike su, amma mun fara da guda 30 tukuna. Yaki da masu yi wa tattalin arziki ta'annati shi ne a gabanmu."

Wannan dai ba shi ne karshen tika-tikan ba, inda a yanzu kwamitin majalisa da ke kula da asusun baitalmalin kasar, na sauraron ba'asi na cibiyoyin gwamnati 22 da ake zargi da wadaka da kudin gwamnati sama da shekaru biyu da suka gabata. Juvenal Nkusi, shi ne shugaban wannan kwamiti:

Yaki da cin hanci bai bar kowa ba a Ruwanda

"Abin da mamaki cibiyar da ke sauraron wannan ba'asi ita ce kuma ta handame babban kaso na kasafin kudin kasa. A duk loakcin da aka yi tunanin me ya sa har yanzu ba mu sauyi ba, baka iya samun tsayayyar amsa. Sannan akwai batun rashin ingancin wasu cibiyoyin shugabanci da ke bukatar kwaskwarima a cikin gaggawa, sannan akwai wasu cibiyoyi da ke mamaye da cin hanci musammn a harkar saye-da sayerwa na wasu kadarorin gwamnati. Akwai batun manyan ayyuka da suka wuce wa'adin kammalawa, wanda kuma ke haddasa mumunar asara."

 A yanzu dai, a yunkurin ta na shafe ayyukan cin hanci da rashawa a Ruwanda, hukumar bincike da sauraron koken jama'a, na aiki hannu da hannu da ma'aikatar Ilimi na ganin an shigar da darusan haramta cin hanci a cikin tsarin makarantun kasar.