Yajin aikin Matuka jiragen kasa a Jamus | Labarai | DW | 04.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin Matuka jiragen kasa a Jamus

Shugabar gwamnatin Jamus ta jaddada bukatar sasantawa, a wani mataki na dakatar da yajin aikin mako guda da matuka manyan jiragen kasa suka fara.

Angela Merkel ta ce 'yancin shiga yajin aiki halal ne a nan Tarayyar Jamus, sai dai matakin matuka manyan jiragen zai yi mummunar tasiri ga 'yan kasuwa da harkoki na tafiye tafiyen jama'a. A kan haka ne shugabar gwamnatin ta yi kira ga masu shiga tsakanin kungiyar direbobin da masu daukarsu aiki, da su gaggauta warware wannan matsalar.

Sai dai shugaban kungiyar matuka jiragen na GDL Claus Weselky, ya yi watsi da shiga tsakani a matsayin mafita daga wannan rikici da ya jagoranci yajin aiki, inda ya dora alhakin yajin aikin akan kamfanin jiragen kasa na deutsche Bahn.

A wannan Lahadin ce dai kungiyar matuka jiragen suka yi kira yajin aikin da za'a fara cikin daren yau zuwa ranar Lahadi da safiya, sai dai tuni jiragen jigilar kaya suka fara nasu yajin aikin da misalin karfe uku na ranar yau, Litinin.

Rahotanni na nuni da cewar yajin aikin zai janyo asarar tsabar kudi euro miliyan 100 a kowace rana.