Yajin aikin likitoci ya ta′azzara lamura a Najeriya | BATUTUWA | DW | 06.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Yajin aikin likitoci ya ta'azzara lamura a Najeriya

Al'umomi a Najeriya, na ci gaba da zama cikin fargaba sakamakon yajin aikin da kananan likitoci suka shiga, lamarin da wasu ke ganin zai kara ta'azzara lamura a fannin kiwon lafiya.

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa a Najeriya ce ta shiga wannan yajin aiki domin nuna turjiyarta bisa yadda gwamnatin tarayyar kasar ta gaza cika musu wasu alkwura da ta dauka. Kungiyar ta ce ko kadan yajin aikin na bana bashi da alaka da karin albashi, sai dai na a sha ruwan tsuntsuye da ake musu da albashi.

A cewar kungiyar dole ce ta sa ta tafiya wannan yajin aiki musamman a wannan lokaci da ake cikin fargabar bullar musamman zazzabin Lassa. Bayanai na cewa a asibitin koyarwa na malam Aminu Kano da kuma asibitin kashi na Dala wadanda ke da muhimmanci ga jama'ar jihar Kano da kewaye, in da marasa lafiya ke cikin garari ba tare da samun kulawar likitoci ba.

Ärzte kämpfen weiter um das Leben des Lassa-Patienten (picture-alliance/dpa)

Malaman jinya da mai zazzabin Lassa

Bullar zazzabin Lassa a arewacin Najeriya wadda har ta kai wacce ta kamu da zazzabin ta rasu ya sanya wasu fargabar cewar talakawa ka iya samun kansu cikin rudani. Sai dai Malam Abdullahi Isma'il Kwalwa, shi ne mukaddashin shugaba a ma'aikatar lafiya ta jihar Kano, ya ce babu wata fargaba duk da zazzabin na Lassa.

Sauti da bidiyo akan labarin