Yajin aikin kafafan yada labarai a Nijar | Siyasa | DW | 05.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yajin aikin kafafan yada labarai a Nijar

A ranar Litinin din nan ce wasu kafafen yada labaru na rediyo da talabijin masu zaman kansu a Jamhuriyar Nijar sun shiga yajin aiki don nuna yadda masu iko ke gallaza masu.

Kalmar "Non a l'assasintant de la presse indepandante au Niger" da harshen Faransa da ke nuni karara da cewar bamu aminta da gallazawar da ake yi wa kafafen yada labaru masu zaman kansu ba, wadannan dai su ne wasu manya- manyan kalaman da suka maye gurbin shirye -shiryen wasu daga cikin kafafen yada labaru masu zaman kansu na gidajen rediyo da talabijin da ke birnin Niamey biyo bayan wata zanga-zangar da masu gidajen kafafen da ke zaman kansu suka shiga.

Gwagwarmayar kafafen dai ta samo asali ne biyo bayan yanke hukuncin aika wasu jami'an bincike a kafafen na yada labaru inda za su binciki takardun harajin gidajen rediyon da talabijin galibi na masu caccakar gwamnati har na tsawon shekaru hudu zuwa biyar da suka gabata, lamarin da ya kai ga masu kafafen cewa tura ta fara kai bango.

Malam Moussa Aksar Jagoran wata jarida mai zaman kanta ne da ake kira Evenement ya ce gwamnati ta yi niyar kashe duk wasu kamfanoni masu zaman kansu na sadarwa da basu mata amshin shata.

Symbolbild Medien in Niger (DW/Bilderbox.com)

A ranar 30 ga watan jiya ne dai ma'aikatar karbar lamho da haraji da ke karkashin ofishin ministan kudin kasar ta aike wasikun ga wasu kafafen wanda tun daga ranar ta nuna cewar a ranar bakwai ga wannan watan ne tawagoginta za su shiga gida-gida na kafafen yada labarun domin aikata binciken takardun da kuwa suka zowa kafafen a karkace.

Malam Diallo Boubakar Jagoran 'yan jarida ne mai fafatukar kwatar hakkokinsu a Nijar, ya tabo tsoma bakin gwamnatin a harkokinsu inda ya ce "Mu tun fil azal akwai yadda muke zabe saboda kungiyoyi ne ke taro su zabi wadanda suke so daga baya sai mu turawa gwamnati zaben da muka yi sai gashi kuma yanzu wai an kafa wani kwamiti da zai karbi 'yan takara daga wani wuri kenan wannan ya sabawa kundin tsarin mulki domin shi kundin ya fayyace yadda ake zaben.

Duk kokarin wakilinmu domin jin tabakin hukumomin kasar kama daga na fannin ma'akatar ministar kudi da tattalin arziki har zuwa ga ta ma'aikatar ministan sadarwa hakarsa ta ci tura.

Kafafen dai sun kuma ambata jingine duk wasu labarai da suka shafi gwamnati ko ma'aikatun gwamnatin kasar kama daga Litinin din nan face sai gwamnatin ta dawo akan turba daga abin da suka kira muzgunawar da suke fuskanta ko wace rana.

Sauti da bidiyo akan labarin