Yajin aiki a Zimbabwe bai samu karbuwa ba | Siyasa | DW | 03.04.2007
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yajin aiki a Zimbabwe bai samu karbuwa ba

Da alamun cewa yajin aiki da kungiyoyin kodago suka kira a Zimbabwe bai tasiri ba yayinda harkoki ke tafiya kamar yadda suke

default

:.Rahotanni daga birnin Harare sunce motocin haya suna ci gaba da zirga zirgansu yayinda kuma ofishin aikewa da wasiku da bankuna da ofisoshin gwamnati,kantuna da shaguna suke gudanar da harkokinsu kamar na kullum a Harare.

Wasu maaikatan dai sunce ba zasu yarda a rage masu albashi ba tunda a cewarsu yanzu ma suna zama ne hannu baka hannu kwarya.

Wata mai saida kaya a wani kanti a birnin Harare,Alice Ushe tace ubangidanta yayi masu barazanr rage kudin albashinsu kwanaki 2 a duk ranar da basu zo aiki ba,saboda haka a cewarta ba zata farantawa alumma rai ta bar iyalinta ba abinci ba,duk da cewa albashin da take karba bai taka kara ya karya ba.

Kodayake da alamun yajin aikin yafi tasiri a wasu masanaantu inda wasu kanfanoni suka ki budewa wanda ya maida yankunan kamar ranar lahadi ne ba baa aiki.

Akwai burbushin yan sanda barbaje da kuma shingaye da aka kafa akan titunan birnin Harare da kuma hanyoyin shiga birnin.

Mai magana da yawun yan sanda Wayne Bvuzijena tun a ranar litinin tayi gargadin cewa zaa girke jamian tsaro a koina cikin birnin

tana mai suka ga tabarbarewar tattalin arzikin kasar da kuma rashin kayaiyakin jin dadin jamaa da hauhawar farashin kayayiyakin masarufi da rashin aikin yi.

Kashi 80 cikin dari nay an kasar Zimbabwe basu da aikin yi yayinda farashin kaya sukayi tashin gwaron zabi inda suka nunka da kashi 1,730 hauhawar farashi da yafi kowanne a duniya.

Jamaa da dama suna zargin shugaba Mugabe dan shekaru 83 da haihuwa da laifin saka kasar cikin matsalolin siyasa da tattalin arziki.

Yajin aiki da aka kira a baya a kasar basuyi tasiri ba yayinda yan sanda suke dakushe shi kafin ya kai koina tare da tsare shugabanin kodago da azabtar da wasu.

A daya hannun kuma maaikata suna tsoron rasa aiyukansu baki daya.

 • Kwanan wata 03.04.2007
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Btvt
 • Kwanan wata 03.04.2007
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Btvt