Yajin ƙin cin abincin fursunonin Falasɗinu | Labarai | DW | 24.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin ƙin cin abincin fursunonin Falasɗinu

Kimanin Fursunoni dubu uku suka yanke shawarar ƙin cin abinci a domin nuna baƙin cikin mutuwar wani Fursuna da suke zargin hukumomin Israila da kisarsa

Domin nuna baƙin cikinsu ga mutuwar wani ɗan Falasɗinu da ke ɗaure a Israila, dubban fursunonin Falasɗinun da ke wurin sun shiga wani yajin ƙin cin abinci.

Kimanin Fursunoni dubu uku suka yanke shawarar ƙin cin abinci a wannan lahadin kamar yadda mai magana da yawun hukumar da ke kula da gidajen yari ya bayyana.

A bayanin da hukumomin Israila suka bayar, sun ce kwatsam sai wani magidanci mai shekaru 30 na haihuwa ya rasu ranar asabar, a ɗaya daga cikin gidajen kason da ke arewacin Israila, kuma suna kyautata zaton cewa bugun zuciya ce.

To sai dai a ɓangaren Falasɗinawan suna zargin cewa ya mutu ne sakamakon wahalan da ya sha wajen wani bincike.

Tuni dai Shugaban Falasɗinu Salam Fajjad ya buƙaci da a gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar wannan mutumi.

Ƙungiyoyin magoya bayan wadanda ke ɗaure a hanun Israila sun ƙaru, suna kuma kira da a bi bayan Falasdinawa huɗun da suka shafe suna yajin ƙin cin abincin.

A wajen arangama da dakarun Israila a gaɓar tekun yamma da kogin Jordan masu zanga-zangar Falasdinu aƙalla 100 suka yi rauni

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita : Zainab Mohammed Abubakar