Yahya Jammeh ya ce ba zai sauka ba | Labarai | DW | 21.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yahya Jammeh ya ce ba zai sauka ba

Shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh ya kara jadada cewar ba zai sauka daga mulki ba tare kuma da yin watsi da kayen da ya sha a zaben shugaban kasar da aka gudanar a cikin wannan wata.

Jameh wanda ya yi jawabi ta gidan talbijan na kasar  ya kuma yi kakkaua sukka ga Kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS wacce ta yi gargadin yin amfani da karfin dawo-dawo domin korarsa daga mulki.Tun da farko dai shugaban na Gambiya  ya amince ya sha kaye amma kuma daga bisani ya yi kira da a sake gudanar da zaben.

A cikin wata Janerun ne na sabuwar shekara yakamata wa'addin mulkin Jammeh ya kammala, sai dai ya ce ba zai mika mulkin ba ga mutumin da ya lashe zaben na shugaban kasa watau Adama Barow wanda ya samu kusan kishi 43 cikin dari na kurin da aka kada.