1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu bore sun sha fitsarinsu a Chadi

January 25, 2023

Daya daga cikin matasan da suka yi wa gwamnatin Chadi bore a watan Oktobar da ya gabata ya yi wa 'yan jarida karin haske a kan irin ukubar da aka gana musu bayan da dakarun gwamnati suka kama.

https://p.dw.com/p/4Mf4L
Hoto: imago/CHROMORANGE

Nadjilem wanda ba sunan shi ne ba ne na asali ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, cewa kwana biyu aka kwashe ana tafiya da su zuwa gidan kason Koro da ke cikin dajin Chadi a cikin mota kirar akori-kura wacce ta rika bude su da kasa ba tare da ruwan sha ko abinci ba, lamarin da a cewarsa ya sa wasu daga cikinsu shan futsarinsu a sakamakon zafin rana da aka yi a lokacin.

Wadannan bayanai dai na fitowa ne bayan da gwamnatin sojojin ta Chadi ta fara sakin wasu daga cikin masu zanga-zangar da take tsare su.

Tun da farko dai matasan sun yi wa gwamnatin Chadi zanga-zanga kan yunkurin shugaban gwamnatin mulkin soji Mahamat Idriss Deby na tsawaita zamansa kan karagar mulki da shekaru biyu ba tare da an gudanar da zabe.