Yaƙi yayi muni a gabashin Yukren | Labarai | DW | 27.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaƙi yayi muni a gabashin Yukren

Hukumomin tsaro na Yukren sun ce sun ƙwaci iko da filin saukar jiragen sama na garin Donetsk da ke a yankin gabashi.

Lamarin ya biyo bayan gumurzun da aka kwashe lokaci mai tsawo ana sha na zin bata kashi tsakanin sojojin gwamnatin da na 'yan aware masu goyon bayan Rasha. Magajin garin na birnin Donetsk, ya ce a ƙalla an kashe mutane 40, biyu daga cikin su farar hula, kuma kowane daga cikin ɓangarorin biyu ya samu asara ta rayukan jama'a.

Jiragen sama na yaƘi waɗanda ke rufawa sojin ƙasa na gwamnatin Yukren baya, sun kwashe daren jiya suna ɓarin wuta a birnin. Shugaban ƙasar Rasha dai ya yi kiran da a dakatar da bude wuta.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman