Yaƙi da cutar masassarar tsuntsaye a ƙasar Jamus | Labarai | DW | 03.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaƙi da cutar masassarar tsuntsaye a ƙasar Jamus

Ministan ayyukan gona na ƙasar Jamus Horst Seehofer yace maáikatar sa za ta dauki wasu kwararan matakai da nufin kare yaɗuwar cutar murar tsuntsaye a ƙasar. Ministan yace a halin da ake ciki, hukumomi na duba yiwuwar taƙaita kai komon jamaá a gonakin kiwon kaji inda aka sami ɓullar cutar a Jamus. A waje guda kuma, jamián kiwon lafiya sun tabbatar da ƙwayar cutar H5N1 a jikin wata mage da ta mutu a tsibirin Rügen dake arewacin Jamus. A Ɓangare guda, Jamián kiwon lafiyar dabbobi na ƙungiyar tarayyar turai sun shawarwaci masu dabbobi na cikin gida, su killace dabbobin na su waɗanda suka hada da mage da karnuka musamman a yankunan da aka sami bullar cutar ta masassarar tsuntsaye.