Yaƙar kwarara zuwa birane | Learning by Ear | DW | 11.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Learning by Ear

Yaƙar kwarara zuwa birane

A yayin da ƙaura zuwa birane daga karkara ke ci gaba da haɓaka, unguwannin manyan birane na neman batsewa saboda yawan jama’a.

default

Wasan kwaikwayonmu zai nunar da yadda wannan cunkoson ya sanye wasu komawa ƙauyensu.

Wasu kan tafi manyan biraren ne idan aka rasa madogara a karkara. Sai dai ba abu ma sauƙi ba ne ka samu mafaka a manyan biranen Afirka da ke cunkushe. Amma sai ka isa birnin, kake sanin cewar hangen Dala ba shiga birni ba ne.

Shirinmu na Ji ka ƙaru, za ku ji labarin abokanai guda uku da suka sauke karatun jami'a ba tare da samun madafa a birni ba, suka koma ƙauyensu domin kafa gamayyar bunka harkokin noma.

Akwai kalubale da ke jiransu, domin gwajin wannan manufa nasu. Ina za su samu kuɗaɗen da za su aza tubalin wannan shiri nasu? Yaya mazauna ƙauyen za su marabci wannan shiri na su? Kuma ko shin wane irin amfanin gona ne ya fi muhimanci a zuba masa jari don gaba, kazalika mai riba? Ka ba mu aron ƙunnuwanka domin jin labarin waɗannan matasa.

Ana iya sauraron shirin Ji Ka ƙaru a harsuna shida: Turanci, Kiswahili, Faransanci, Hausa, Portugis da Amharik. Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ke tallafawa shirin.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin

Kwafa