Xi Jinping ya gana da shugabannin Turai | Labarai | DW | 26.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Xi Jinping ya gana da shugabannin Turai

Shugaban kasar Chaina Xi Jinping ya gana da shugabannin tarayyar Turai, yayin da bangarorin biyu ke neman hanyoyin bunkasa dangantaka da Chaina tare da matsa mata lamba game matakanta na kasuwanci.

Ganawar wadda ta gudana a wannan Talatar a birnin Paris ya sami halartar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban hukumar tarayyar Turai Jean-Claude Juncker da shugaban Faransa Emmanuel Macron dan ba ne na shirya taron koli tsakanin kungiyar tarayyar Turai da Chaina.


Da yake jawabi a taron manema labarai na hadin gwiwa shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga takwaransa na Chaina Xi Jinping ya martaba hadin tarayyar Turai tare da bukatar karfafa dangantaka tsakanin su.


"Muna so mu cigaba da gina dangantaka mai karfi a tsakanin kasashe. Muna da banbance banbance a tsakanin mu, a tarihin dan Adam baka raba shi da nuna karfin tasiri a yayin gogayya, dukkanin mu babu wanda bashi da kwarewa to amma muna girmama Chaina muna kuma da kwakkwarar kudiri na cigaba da tattaunawa da hadin kai. Muna sane da cewa manyan abokan mu suna girmama hadin tarayyar Turai da al'adunta da kuma matsayinta a idanun duniya."