Wutan jeji a kudancin Califonia | Labarai | DW | 25.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wutan jeji a kudancin Califonia

Yanayi na sanyi da da iska na taimakawa jamian kashe gobara samun nasarar shawo kann wutar jeji,dake cigaba da cin yankinmkudancin Califonia ,a tsawon kwanaki 5 da suka gabata.Kawo yan yanzu dai wannan wutar jeji dake cigaba da ruruwa a wannan jiha da Amurka,ya haifar da asara na katankwacin dala billion guda,ayayinda ya tilasta mutane sama da million guda tserewa daga gidajensu.Shugaba George W Bush dake kann hanyarsa ta zuwa Califonian yace...

„“Zan tabbatarwa da mutanen califonia cewar,gwamnatin tarayya zata tura dukkan tallafi da ake bukata na kudi da kuma mutane,domin taimaka wajen kashe wannan wuta.kazalika zan tabbatar musu dacewar,saboda yarjejeniyar dana rattaba hannu akai jiya ,akwai tallafi wa jama’ar Califonia“.

Kawo yanzu dai mutane 5 ne suka rasa rayukansu,ayayinda wasu 80 suka jikkata ,sakamakon wannan wuta.