Wilder ya yi nasarar dambe karo na 39 | Zamantakewa | DW | 08.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Wilder ya yi nasarar dambe karo na 39

Shahararren dan damben zamanin nan dan kasar Amirka Deontay Wilder, zakaran duniya a fagen masu nauyi ya doke abokin karawarsa Bermane Stiverne na kasar Kanada tun a turmin farko.

A karshen mako ne 'yan danben biyu suka cire reni a birnin New York na kasar Amirka, wannan dai ita ce nasara ta 39 da Deontay Wilder mai shekaru 32 ya samu a karawa 39, sai dai kammala karawar tasu ke da wuya nan take Wilder ya kalubalanci shahararren dan demben zamaninin nan dan kasar Birtaniya Anthony Joshua dan asalin kasar Najeriya, wanda ya ce ya zabi ranar da ta yi masa dai dai domin su kara da juna.