1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: Yara miliyan 115 ke bukatar allurar Polio

Yusuf Bala Nayaya
March 23, 2017

Matsalar tsaro da ke addabar wasu kasashe ciki kuwa har da Najeriya na daga cikin abin da ke zagon kasa ga kokari na kawar da Polio.

https://p.dw.com/p/2Zqsw
Nigeria Polio-Impfung
Hoto: Global Polio Eradication Initiative

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ta kudiri aniya ta yin allurar rigakafin cutar shan inna ko Polio ga yara miliyan 115 a wasu kasashe na Afirka a mako mai zuwa. Wannan na zuwa a kokarin hukumar na kawar da wannan cuta da ke nakasa yara a duniya.

A cewar jawabin na cibiyar kula da lafiyar ta Majalisar Dinkin Duniya yara 'yan kasa da shekaru biyar ne za a yi musu wannan rigakafi, inda ma'aikata masu digon allurar rigakafin Polio sama da 190,000 za su karada a kasashe 13 daga Tsakiyar Afirka da Afirka ta Yamma ciki har da kasashen Najeriya da Kwango da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Yaki da cutar ta Polio dai na bukatar rigakafin ga yara sama da kashi 90 cikin dari da ka iya kamuwa da cutar a kasashen da ke da wannan cuta, abin da ke samun nakasu sakamakon matsalar tsaro da ke addabar wasu kasashe ciki kuwa har da Najeriya, wacce bayan bayyana kasar cikin marasa cutar Polio ta sake bulla da mai da hannun agogo baya. Kasashen da ake samun cutar na bazuwa su ne Najeriya da Pakistan da Afghanistan.