1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO ta yi gargadi kan zuzuta cutar Corona

February 3, 2020

Hukumar Lafiya ta Duniya ta nuna rashin jin dadi kan yadda ake yada labarai da ke cin karo da juna game da cutar numfashi ta cornonavirus, wadda ke ci gaba da hallaka rayuka.

https://p.dw.com/p/3XCo3
Coronavirus - Illustration
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/Centers for Disease Control and Prevention

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, WHO, ta ce tana aiki ka’in da na’in da kamfanonin sadarwar Intanet saboda yaki da karairayin da wasu ke yadawa dangane da cutar nan ta coronavirus da ta addabi China da wasu kasashen duniya.

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi gargadi kan hadarin da ke tattare da yada labarai marar tushe game da cutar, wadda a yanzu ta hallaka rayukan sama da 360 a China.

Wannan matsayi na WHO, na zuwa ne daidai lokacin da China ke zargin Amirka da zuzuta matsalar, da kuma ke tayar da hankali a duniya.

A wannan Litinin ne kuma hukumomi a Wuhan na China inda cutar ta bulla, suka kaddamar da wani sabon asibiti da aka gina cikin kwanaki 10, musamman saboda kula da wadanda ke fama da wannan cuta.

Sama da mutum dubu 17 da 300 ne dai suka kamu da cutar a kasar ta China, yayin kuma da ake da wasu daidaiku a wasu kasanshen.