WHO ta gamsuwa da rigakafi cutar Ebola | Labarai | DW | 29.05.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

WHO ta gamsuwa da rigakafi cutar Ebola

Mataimakin Darakta mai kula da agajin gaggawa na Hukumar Lafiya ta Duniya Dakta Peter Salama ya bayyana gamsuwarsa tare da kyakykyawan fatan samun nasarar rigakafin cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango.

Dakta Salama ya bayyana hakan ne yayin da hukumar ta samu nasarar yi wa kashi chasa'in na mutanen da suka yi ta'ammali da wadanda suka kamu da cutar Ebola a Kwango allurar ta rigakafi. Daga nan sai ya kara da cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na duba yiwuwar fara amfani da wasu magungunan gwaji guda biyar na cutar ta Ebola a fadin kasar ta Kwango.