WHO ta ce za a samun allurar cutar Zika | Labarai | DW | 12.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

WHO ta ce za a samun allurar cutar Zika

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ko OMS ta ce cibiyoyin binciken kimiyya kimanin 15 a yankuna daban-daban na duniya sun dukufa wajen samar da allurar yaki da cutar Zika.

Mataimakiyar babban daraktan hukumar ta WHO Dokta Marie-Paule Kieny wacce ta tabbatar da hakan lokacin wani taron manema labarai da ta kira, ta ce yanzu haka dai akwai wasu allurai guda biyu wadanda cibiyar kiwon lafiya ta Amirka da kuma wata cibiyar bincike ta kasar Indiya suke aiki kansu da kuma ake da kwarin gwiwar samun nasara. Sai dai kuma ta ce duk da irin ci gaban da aka samu a cikin binciken, za a dauki akalla watanni 18 nan gaba kafin a soma aiki da allurar a matakin gama gari. Haka zalika Dokta Marie-Paul Kieny ta ce masu aikin binciken za su bukaci makwanni hudu zuwa takwas a nan gaba domin tan-tance alakar da ke da akwai tsakanin kwayar cutar ta Zika da kuma jarirai masu nakasa da mata masu juna biyu da suka kamu da cutar suke haifa dama kuma matsalar jijiyoyin da wasu mutanen da sauron da ke dauke da kwayar cutar ta zika ya ciza suke fuskanta.