WHO ta ce mutane dubu 10 sun kamu da Ebola | Labarai | DW | 25.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

WHO ta ce mutane dubu 10 sun kamu da Ebola

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce yanzu haka yawan da suka kamu da cutar nan ta Ebola sun haura mutum dubu 10, galibinsu su a Liberiya da Saliyo da kuma ƙasar Gini.

Hukumar dai ta fidda waɗannan alƙaluman ne a wannan Asabar ɗin dai dai lokacin da ta bayyana cewar waɗanda cutar ta yi ajalinsu sun kai kusan dubu biyar kuma yawansu ka iya ƙ-aruwa. Wannan dai na zuwa ne dai dai lokacin da WHO ɗin ta ce ta fidda wani tsari da zai taimaka mata wajen gaggauta samar da magungunan rigakafin cutar ta Ebola.

Guda daga cikin manyan jami'an hukumar Marie-Paule Kieny ta ce nan da watan Disamba ake sa ran komai zai kankama dangane da wannan yunkuri da suke yi.