WHO ta ce akwai yiwuwar samun allurar riga-kafin Corona a shekarar 2021 | Labarai | DW | 20.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

WHO ta ce akwai yiwuwar samun allurar riga-kafin Corona a shekarar 2021

Yanzu haka akwai fiye da samfur guda 20 na alluran riga-kafin cutar Corona da ake gwajin ingancinsu a asibitoci da wasu cibiyoyin binciken kimiyya.

Hukumar lafiya ta duniya WHO na da yakinin cewa a tsakiyar shekara ta 2021 za a samu allurar riga-kafin cutar Corona, kamar yadda aka ji shugaban sashen masana kimiyya ta hukumar, Soumya Swaminathan na fada a cikin wata hira da kamfanin dillacin labarun Jamus na DPA.

 

Yanzu haka akwai fiye da samfur guda 20 na alluran riga-kafin cutar da ake gwajin ingancinsu a asibitoci da ma wasu cibiyoyin binciken kimiyya. Saboda haka hukumar ta WHO na da kyakkyawan fata cewa za a iya yin nasarar amfani da wasu daga cikin alluran riga-kafin.

A halin da ake ciki kuma gwamnatin tarayyar Jamus ta sanar cewa ta kara yawan kasafin kudin tallafi na binciken magani da jinyar cutar daga Euro miliyan dubu 15 zuwa miliyan dubu 45.