1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: Ebola na iya yaduwa daga Kwango

October 18, 2018

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce akwai yiwuwar samun yaduwar kwayar cutar nan ta Ebola da ke barna a halin yanzu a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, zuwa wasu kasashe makwabta.

https://p.dw.com/p/36mXs
Demokratische Republik Kongo | Ebola
Hoto: Getty Images/J. Wessels

Hukumar ta lafiya ta fadi hakan ne lokacin da tawagar kwararrunta na kimiyya ke nazarin ko suna iya bayyana cutar a Kwango a matsayin matsalar gaggawa ta lafiya a duniya.

Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana tsananin damuwarta game da halin da ake ciki, kuma kamar yadda ta ke nunawa, za ta yi dukkanin mai yiwuwa don ganin an dakile cutar.

A halin da ake ciki ma dai ma'aikatar lafiya a Kwangon, ta sanar da sabbin alkaluman mutum uku da cutar ta kashe a kasar, abin da ya kai ga adadin mutum 142 da suka salwanta ke nan jimilla a arewacin lardin Kivu.