1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

WHO: Ana samun karuwar mace-macen mata

Binta Aliyu Zurmi
February 23, 2023

Hukumar lafiya ta Malajisar Dinkin Duniya WHO a wani sabon rahoton da ta fidda ta ce a kowane mintuna biyu a kan sami mace daya da ke rasa ranta bisa lalurori da suka shafi daukar ciki da kuma haihuwa.

https://p.dw.com/p/4Nrsm
Tedros Adhanom Ghebreyesus | Generaldirektor der Weltgesundheitsorganisation WHO
Hoto: Martial Trezzini/KEYSTONE/picture alliance

A shekarar 2020 sama da mata dubu 280 ne suka rasa rayukansu ta wannan hanya, kusan mata dari 800 ke nan a kowace rana a fadin duniya. Adadin da ke nuni da raguwar matan da ke rasa rayukansu daga matsalolin da likitoci da dama suka ce za iya kauce ma wa a shekarun baya.

A rahoton nata na wannan Alhamis ya nuna an fi samun asarar rayukan matan ta hanyar juna biyu ko kuma wajen haihuwa a kasashen da ke kudu da hamada sahara.

Nan da shekarar 2030 a muradun Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba mai dorewa ana fatan rage yawan mace macen matan da kusan kaso 70 cikin dari.