WHO: An kawar da annobar Polio a Najeriya | Labarai | DW | 26.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

WHO: An kawar da annobar Polio a Najeriya

Hukumar Lafiya ta Duniya ta cire Najeriya daga sahun kasashen da ke fama da Polio bayan da aka shafe fiye da shekara guda ba tare da samun wanda ya kamu da cutar ba.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce Najeriya ta fita daga sahun kasashen da cutar Polio ta zama annoba bayan da kasar ta shafe sama da shekara guda ba tare da samun wanda ya kamu da cutar ba.

WHO din ta bayyana hakan ne a wani taron da aka gudanar a Amirka kan cutar ta Polio inda ta ce wannan matsayin da Najeriya ta kai babbar nasara ce, kuma wani mataki ne na sanya Afirka cikin jerin nahiyoyin da suka kama hanyar kawar baki daya.

Hukumar ta ce in har Najeriya ta shafe tsawon shekaru uku ba tare da sake bullar cutar ba, to za a ayyana kasar a matsayin wadda ta kawar da ita baki daya.

Yanzu haka dai Afghanistan da Pakistan ne a duniya suka rage a matsayin kasashen da cutar ta Polio ta zama annoba.