Wayar da kan al′umma a Nijar | Himma dai Matasa | DW | 23.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Wayar da kan al'umma a Nijar

Kafafen yada labarai mallakar al'umma da ke wayar da kan jama'a wadanda ke a yankuna daban-daban, kan gudanar da shirye-shirye iri-iri kama daga tallace-tallace domin taimakon al'umma.

Al'ummar Nijar na cin gajiyar kafafen yada labarai

Al'ummar Nijar na cin gajiyar kafafen yada labarai

Wata mai kishin kasa a Jamhuriyar Nijar ta kafa gidan radio domin tallafa wa al'ummar yankinta. Ita dai wannan 'yar kishin kasa mai suna Chatou Mahmadou mamba ce a wata kungiya mai zaman kanta mai suna "Espace Citoyen" a harshen Faransanci. Chatou dai mai rajin kare hakkin dan Adam ne ta hanyar amfani da gidan radiyon domin bai wa al'ummar ciki da wajen birnin Yamai damar tofa albarkacin bakinsu game da abin da ke ci musu tuwo a kwarya. Chatou na kuma yin amfani da gidan radiyon domin yada wasu manufofi na al'umma da ke bukatar canji, hakan ne ya sa ta rika tursasawa hukumomi sauke wasu nauye-nauye da suka rataya a wuyansu na al'umma. Yayin da gwamnati ta rushe wurare a wata unguwa cikin birnin Yamai a Jamhuriyar ta Nijar inda aka rushe wasu gidaje da dama tare da gina wata sabuwar gada da kuma wasu hanyoyi. Yawancin mazauna yankunan sun yi asarar gidajensu, hakan ce ta sa Chatou ta tsaya tsayin daka domin ba mazauna ungawar damar kai korafinsu ga hukumomin da suka dace, tace ta hakan ana samun nasara sosai. Jarumta da kwarin gwiwa suka sa Chatou take fita ta na haduwa da mutane daban-daban, musamman ma marasa galihu domin tallafa musu.

Sauti da bidiyo akan labarin