1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata 'Yar scotland ta kamu da cutar Ebola

Mouhamadou Awal BalarabeDecember 30, 2014

An kwantar da ma'aikaciyar lafiya ta Save the Children a Saliyo a asiti bayan da bincike ya tabbatar da cewa ta na dauke da kwayar cutar Ebola mai saurin kisa.

https://p.dw.com/p/1ED9L
Hoto: Reuters/Neil Hall

Wata ma'aikaciyar lafiya na yankin Scotland ta harbu da kwayar cutar Ebola dake saurin kisa. Tuni ma dai aka kebeta a wannan Talatar bayan da bincike ya tabbatar da ita a matsayin mutum na farko da ya kamu da wannan cuta a Birtaniya.

Ita dai wannan nas ta na yi wa kungiyar agaji ta Save The children aiki ne a kasar Saliyo, inda ake jin cewa ta harbu da kwayar cutar. Za a yi wa daukacin mutane 71 da suka yi mu'amala da ita gwaji don ganin cewa ko sun kamu da cutar ko a'a. Wannan lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake samun yaduwar Ebola a wurare uku a Saliyo..

Alkaluman da Hukumar Lafiya ta duniya ta fitar sun nunar da cewa kusan mutane dubu takwas cutar Ebola ta yi ajalisun a duniya cikin watanni 12 na baya-bayannan, yayin da mutane dubu 20 suka harbu da kwayar cutar ta Ebola.