Wata ′yar kunar bakin wake ta hallaka a Najeriya | Labarai | DW | 26.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata 'yar kunar bakin wake ta hallaka a Najeriya

A birnin Maiduguri da ke a yankin arewa maso gabashin Najeriya wata matar 'yar kunar bakin wake ta hallaka a sa'ilin da ta yi kokarin tayar da bam a tsakiyyar kasuwar sayar da shanu.

Wani jami'in kungiyar agajin gaggawa ta Nema Ibrahim Abdulkadir ya ce mata biyu ne ke dauke da bam, yayin da daya ta tashi da ita ba cikin shiri  ba,ta raunata mutane da dama,kana daya aka kamata kafin ma ta tayar da bam din. Ya kuma ce  yanzu haka mutanen da suka jikkata an garzaya da su zuwa  asibiti inda ake yi musu magani.