Wata sabuwar Badaƙala a kan zare tallafin man fetur a Najeriya. | Siyasa | DW | 20.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Wata sabuwar Badaƙala a kan zare tallafin man fetur a Najeriya.

Wata kotu da ke Abuja ta yanke hukuncin cewar gwamnatin ba ta da izinin cire tallafin kuɗaɗen da ta ke bayarwa akan fetur.

Tun farko da ƙyar da gumin goshi dai aka kai ga shawo kan yan ƙwadagon Tarrayar Najeriyar dama al'ummar ƙasar da suka fito suka ce ba zata saɓu ba game da matakin gwamantin ƙasar na zare tallafin man fetur.

To sai dai kuma ana shirin sake shiga fage ga yan ƙwadagon da a jiya suka kai ga nasarar samun nasara, a hukuncin da wata kotu a Abuja ta bayyana na haramta duk wani yunƙuri na zare tallafin man fetur ɗin, amma kuma gwamantin tace da sauran sake.

Gwamnatin Tarrayar ta ce babbar asara ta ke samu a sakamakon tallafin.

Shugaban ƙasar Goodluck Ebele Jonathan ya ce batun ci-gaban tallafin na zaman ɓarnar kuɗi da asara babba da ƙasar ba zata iya ci-gaba da yi ba. Kasar na yin ƙorafin asarar kusan kaso 30 cikin ɗari na ɗaukacin kasafinta wajen tafiyar da tallafin, da ake zargin na ƙarewa a hannun yan' boko da yan kasuwar da ke hada hadar man fetur.Abin kuma da a cewar Dr Yarima Lawal Ngama dake zaman ƙaramin ministan kudin ƙasar ta Najeriya da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa.

Ya ce ''karfin iya ɗauka ko kuma zare tallafin, ana dai ambato cin hanci a cikin batun na tallafin da ya zamo mattatara ta sakayya ga masu uwa a cikin gindin murhun ƙasar. Wani binciken da aka gudanar ya kai ga shafar wasu manya a cikin jam'iyyar PDP mai mulki, da hannu a karɓar kusan naira Trilliyan ɗaya da miliyan dubu 700 da sunan tallafin amma kuma suna ƙarewa da talafawa aljihunsu.''

Zare tallafin ba zai iya kawo ƙarshen cin hanci ba a cikin sha'anin man fetur.

Kusan shekara guda ana shari'a ba tare da tabbatar da laifi ko da kan ɗaya, daga cikin mutane da kamfanoni kusan 26 da aka ce sunci sun sha da gumin talakawan ƙasar ba.Mallam Salihu Lukman dai na zaman wani masanin tattalin arzikin ƙasar ta Najeriyar, kuma a cewarsa zare tallafin ba yana zaman mafita ga kokarin kawo karshen dattin dake cikin masana'antar man ƙasar ba.Abun jira a gani dai na zaman mafita a cikin sabon rikicin, da ke ɗaukar hankalin al'umma.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto da kuma hirar da Usman Shehu Usman ya yi da Dr Abubakar Muazu, wani mai yin sharhi a kan al'amuran da ke jami’ar Maiduguri, wanda ya yi tsokaci akan batun.

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Abdourahamane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin