1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata jarida ta tona wa Trump asiri

September 28, 2020

Shugaban kasar Amirka ya sake shiga wata sabuwar badakalar da shafi haraji, abin da wasu masu sharhi ke cewa tana iya yi masa lahani a takarar da sake yi a zaben watan Nuwamba.

https://p.dw.com/p/3j6Ne
Trump Coronavirus Press Conference
Hoto: picture-alliance/CNP/A. Drago

Jaridar New York Times ta Amirka ta yi wa Shugaba Donald Trump wata sabuwar bankada, inda ta ce harajin dala 750 ne kacal shugaban ya biya a shekarar 2016 da ya kama ragamar kasar.

Wani babban bugu da karin ma inji jaridar, Mr. Trump bai biya ko da sisin kwabo ba a shekaru 10 cikin 15 din da suka gabata, yana mai jinginewa da hujjar cewa yawan asarar da ya yi a kamfanoninsa ta fi ribar da ya samu a shekarun.

To sai dai fa a wani taron manema labarai da ya yi jim kadan bayan fitowar tonon sililin, Shugaba Trump ya ce wannan labari ne na kanzon kurege, tare ma da zargin cewa hukumar tattara kudaden shigar Amirkar ba ta yi masa adalci.