Wata gobara a asibiti ta kashe mutane da dama a Mosko | Labarai | DW | 09.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata gobara a asibiti ta kashe mutane da dama a Mosko

Akalla mutane 45 sun rigamu gidan gaskiya lokacin da wata gobara ta tashi a wani asibiti, inda ake jiyyar masu fama da matsalolin shan miyagun kwayoyi dake birnin Mosko. Wasu mutum 10 sun samu raunuka yayin da aka ceto mutum 160 daga ginin asibitin mai hawa biyar. In ban da mutum biyu dukkan wadanda gobarar ta rutsa da su mata ne wadanda ake yiwa jiyya matsalolin shan kwaya. Hukumomi a birnin sun ce bankawa asibitin wuta aka yi dagangan. Wani ma´aikacin kwana-kwana ya zargi ma´aikatan asibitin da rashin sanar da jami´an ceto tashin gobarar da wuri. Hakazalika ma´aikatan asibitin ba su dauki wani mataki na kwashe majiyyatan daga asibitin ba lokacin da gobarar ta tashi.