Wata babbar kotu a Libiya ta ce zaɓen Ahmed Maitik bai halarta ba | Labarai | DW | 05.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata babbar kotu a Libiya ta ce zaɓen Ahmed Maitik bai halarta ba

Kotun tsarin mulki ta ƙasar ta aiwatar da hukuncin cewar zaɓen da aka yi na firaministan ba ya kan ƙaida.

An zaɓi Ahmed Maitik makonnin biyun da suka gabata a wata ƙuri'ar da aka kaɗa a majalisar dokokin ƙasar cike da rikici. Wanda wasu 'yan majalisun suka ce addadin da yakamata a samu na waɗanda suka yi zaɓen bai kai mizanin yadda ake so ba.

Ahmed Maitik ya fito ne daga yankin Misrata da ke a yammancin ƙasar, inda ƙungiyoyin masu kishin addini ke da rinjaye, wanda kuma sauran ɓangarorin addinan ƙasar ke yin adawa da shi. Gidan telbijan na ƙasar Libiya ya ce tuni da lauyoyinsa suka ɗaukaka ƙara a kan wannan hukunci.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar