1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wata ƙungiyar lauyoyi na ƙasa da ƙasa za ta ɗaukaka ƙarar sakataren tsaron Amirka mai barin gado, Donal Rumsfeld, gaban kotu a nan Jamus.

November 14, 2006
https://p.dw.com/p/Buc8

Wata ƙungiyar lauyoyin ƙasa da ƙasa, ta ce za ta ɗaukaka ƙarar sakataren tsaron Amirka mai barin gado, Donald Rumsfeld, da wasu manyan jami’an ƙasar gaban kotu a nan Jamus. Ƙungiyar dai na zargin Rumsfeld da jami’an ne da amincewa da azabtad da fursunonin da dakarun Amirkan suka yi, a sansanoni kamarsu gidan yarin Abu Ghraib na birnin Bagadaza da kuma Guantanamo a Cuba, a lokacin da ake tsare da su.

Gaba ɗaya dai, lauyoyin na wakilcin wasu tsoffin fursunonin Iraqin ne guda 11, waɗanda aka taɓa tsarewa a sansanin Abu Ghraib ɗin da kuma Guantanamo Bay a Cuba. Ƙungiyar da ke ɗaukaka ƙarar, ta ƙunshi lauyoyi ne daga nan Jamus da kuma Amirka, waɗanda ke dogaro kan wata dokar Jamus da ke ba da damar gabatad da masu aikata laifuffukan yaƙi a kotunan nan ƙasar, ko’ina ne kuma suka aiakata laifuffukan a duniya.