Wasu sun tsira daga hadarin jirgin saman fasinja a Nijeriya | Labarai | DW | 23.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wasu sun tsira daga hadarin jirgin saman fasinja a Nijeriya

Fiye da kashi 50 cikin 100 na fasinjoji 116 dake cikin wani jirgin saman fasinjan Nijeriya da ya hadari sun tsallake rijiya da baya. Babban jami´in hulda da manema labarai na gwamnatin jihar Oyo, inda jirgin ya fado, wato Adeola Oloko ya ce yanzu haka an umarci dukkan ma´aikatan kiwon lafiya dake yankin da su je wurin da hadarin ya auku don kula da wadanda suka samu rauni. Mai magana da yawon shugaba Olusegun Obasanjo, Oluremi Oyo ta tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta samu rahoton game da wadanda suka tsira daga wannan hadari. Ta ce Allah Ya nuna ikonsa to amma ta ce ba ta san yawan wadanda suka tsallake rijiya da baya ba. To sai dai rahotanni da dumiminsu na cewa kimanin fasinjo 50 sun tsira da ransu. Jirgin saman samfurin Boeing 737 mallakin kamfanin Bellview an daina jin duriyarsa mintuna kalilan bayan ya tashi daga Legas zuwa Abuja. Jirgin ya fado ne a wani yanki dake kusa da Kishi dake cikin jihar Oyo mai nisan kilomita 400 arewa da Legas. Ya zuwa yanzu dai ba wani labari game da musabbabin aukuwar hadarin.