Wasu sojojin Nijar sun mutu a Sahara | Labarai | DW | 03.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wasu sojojin Nijar sun mutu a Sahara

Akalla sojojin Nijar 3 ne suka rasa rayukansu a cikin hamadar Sahara sannan aka ceto wasu 8 da ransu bayan da suka bace a lokacin da suke yin wani sintiri na hana bakin haure ketarawa zuwa Libiya da nufin shiga Turai.

Wakiliyarmu da ke Agadez Tilla Amadou ta ce hukumomi sun ce rashin ruwa ne ya yi sanadiyyar rasuwar sojojin, kuma tuni aka bada sunayensu wadanda suka hada da Sufeto Abdou Brah da Mamane Sani Souley da kuma Daouda Adamou Kondo. Tuni dai gwamnan Agadez Sa'adou Soloke ya kama hanyarsa ta zuwa birnin Arlit don tattaunawa da jami'ai kan wannan lamari. Jihar Agadez dai na zaman guda daga cikin wuraren da 'yan cirani ke amfani da ita a yankurinsu na zuwa Turai.