1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasu matasan Burtaniya na kokarin shiga IS

Ahmed SalisuMarch 15, 2015

'Yan sanda a Burtaniya sun tsare wasu samari uku bayan da aka bankado kokarin da suke yin na shiga kungiya nan ta IS da ke kokarin girka daular Islama a Siriya da Iraki.

https://p.dw.com/p/1ErFg
Syrien IS-Kämpfer
Hoto: picture-alliance/Zuma Press/M. Dairieh

Rundunar 'yan sanda Burtaniya din ta ce ta damke samarin ne wanda shekarunsu ke tsakanin 17 zuwa 19 bayan da aka maida su gida daga Turkiyya inda suke yunkuri na ketarawa Siriya don tallafawa IS a fafutukar da ta ke yi.

Mahukuntan kasar da suka nuna kaduwarsu kan wannan lamari, sun zargi kafofin yada zumunta na Intanet da taimakawa wajen samun saukin sadarwa tsakanin matasa da masu tsaurin kishin addini a Siriya wanda kan ja ra'ayinsu su shiga kungiyar IS.

A dan tsakanin nan matasa kimanin 700 ne daga kasar suka fice don isa Siriya da nufin shiga IS din don ko a kwanakin baya ma sai da wasu 'yan mata uku daga kasar suka fice inda ake zaton sun shiga Siriya ta Turkiyya don hadewa da 'yan IS din.