Wasu makaman Jamus sun yi ɓatan dabo | Labarai | DW | 11.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wasu makaman Jamus sun yi ɓatan dabo

Majiyoyin daga sojojin Jamus sun ba da sanarwa cewar wani akwati da ke tsatsage da makamai a cikinsa ya ɓace a kan hanyarsa ta zuwa Mali.

Makaman sun yi ɓatan dabo ne sama ko ƙasa a cikin watan Mayun da ya gabata a lokacin da aka yi safara makaman ta jirgin sama na kamfanin Air Franceb tare da wata tawagar sojojin na Jamus zuwa Mali.Wani kakkakin rundunar sojojin na Jamus ya tabbbatar wa da jaridar Welt am Sonntag cewar har yanzu suna cikin yin cigiyar makaman.

A ƙarshen watan Mayun da ya gabata ne wata tagar ta sojojin Jamus ta tashi daga birnin Berlin zuwa Mali,cikin jirgin sama na kamafanin sufurin jiragen sama na Air France bayan sun yadda zango a birin Paris.Kuma duk da cewar an yi rejistan sojojin da makaman nasu amma bayan sun sauka a Malin ba a ga makaman ba.Sojojin na Jamus dai na daga cikin sojojin da suke ba da taimakon tabbatar da tsaro a arewacin Malin a cikin rundunar kiyaye zaman lafiya ta MDD watau MINUSMA.