1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Wadatar abinci

Matsalar yunwa a wasu kasashen yammacin Afirka

Gazali Abdou Tasawa SB)(AH
April 5, 2022

Wani rahoton bincike da kungiyar agajin kasa da kasa ta fitar ya nunar da cewa mutane sama da miliyan 27 sun fada matsalar yunwa a kasashen Afirka ta Yamma musamman Jamhuriyar Nijar da Najeriya da Burkina Faso da Mali.

https://p.dw.com/p/49UfK
Nigeria Hungerkrise
Hoto: Chinedu Asadu/AP Photo/picture alliance

Rahoton na kungiyar Oxfam ya ce mutane miliyan 27 ne suka fada yanayin yinwa a kasashen na Afirka ta Yamma. Kungiyar ta OXFAM ta kuma yi gargadin cewa idan har gwamnatocin kasashen da kungiyoyin kasa da kasa ba su gaggauta daukar matakan tunkarar matsalar ba ta hanyar kawo tallafi nan zuwa watan Yuni, to wasu mutanen miliyan 11 za su fada su ma a cikin matsalar yinwar. Wanda zai sa Adadin mutanen da yinwar ta shafa  zai tashi mutum miliyan 38 kuma kananan yara ‚yan zuwa shekaru shida kusan miliyan shida da rabi za su kamu da tamowa. Malam Djibo Bangna shugaban kungiyar mutanen karkara ta Plate Forme Paysane ya tabbatar da wannan matsala.

Südsudan l Krise l Hunger - Kinder in Juba
Hoto: Tony Karumba/AFP via Getty Images

Gwamnatin kasar Jamhuriyar Nijar da kanta ma dai ta tabbatar da cewa akwai mutane tsakanin miliyan hudu zuwa shida da suke fuskantar matsalar karancin abinci a kasar a shekarar bana a sakamakon matsalolin karancin ruwan sama da ta tsaro a shekarar ta bana. A kann haka ne ta sanar da kaddamar da wani shiri na wucen gadi na kawo tallafi ga talakawa musamman a yankunan da suka yi fama da tsaro.

To sai dai Malam Diori Ibrahim mai kula da harkokin karancin abinci da rayuwar mutanen karkara a kungiyar alternative espace citoyen ya ce hanyar da kusan kullum gwamnatin Jamhuriyar Nijar ke dauka domin tunkarar matsalar karancin abinci a kasar ba mai billewa ba ce.

Kungiyoyi da dama dai na bayar da shawarar cewa hanya mafi a ala da ya kamata kasa kamar Nijar ta bi wajen shawo kan matsalar karancin abinci da ta zamo tamkar ta gado a kasar, ita ce mai da hankali ga bunkasa noman rani ta la'akari da yadda nazari ya nunar da cewa arzikin ruwa na karkashin kasa da Allah ya huwace wa kasar ya fi na Afirka gaba daya in an hade shi waje daya.