Wasu kasashe na nuna damuwar su kan rashin halartar Iran a taron Geneva | Labarai | DW | 22.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wasu kasashe na nuna damuwar su kan rashin halartar Iran a taron Geneva

A yayin da aka soma babban taron Geneva kan batun kasar Siriya, kasashe da dama na cigaba da cece-kuce sakamakon haramta wa Iran shiga wannan zauren taro.

Kasar Rasha dai ta fito karara ta nuna rashin gamsuwarta kan wannan mataki, yayin da kasar ta Iran ta ce su sani cewa sun yi babban kuskure kuma ba za su ci nasara kan wannan taro ba, muddin dai babu kasancewar ta wurin.

Tuni al'ummar Siriya da suka kosa da yakin basasan da ya ki ci ya ki cinyewa a kasarsu, ke fatan ganin wannan taro ya haifar da tsaida wuta cikin wannan kasa dake fama da rikicin tawayen da ya haddasa rasuwar mutane fiye da dubu dari da talatin, yayin da wasu akalla mutane dubu dari biyar suka ji rauni. Sannan wasu miliyoyi suka rasa matsugunnansu a wannan kasa, wadda daga batun juyin-juya hali ta fada ga yakin basasa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Mohammad Nasiru Awal