Wasu jami′an gwamnatin Najeriya sun mutu a hatsarin jirgin sama | Labarai | DW | 16.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wasu jami'an gwamnatin Najeriya sun mutu a hatsarin jirgin sama

Gwamnan jihar Kaduna Patrik Ibarhim Yakowa da wasu muƙarrabansa sun rasu, a hatsarin jirgin sama cikin jihar Bayalsa

Gwamnan jihar kaduna da ke a yankin arewacin Tarrayar Najeriya Patrick Ibrahim Yakowa da tsohon mai bai wa shugaban ƙasar shawara a kan al'amuran tsaro janar Azazi Allah ya yi masu cikawa a wani hatsarin jirgin sama da ya auku.

Hukumomi sun ce mutane a ƙalla guda shidda suka mutu a cikin hatsarin da wani jirgin saman soji mai saukar ungulu ya yi da su a jihar Bayalsa. Shugaban ƙasar ta Najeriya ya ba da ummarnin da a gudanar da binciken gaggawa domin gano dalilan hatsari. Wannan dai shi ne karo kusan na barkatai da ake fama da hatsarin jirgin sama a Najeriyar, wanda a cikin sa a kan samu asaran rayukan jama'a.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Usman Shehu Usman